Tace lamarin ya tabarbare dalilin rashin ingantattun kayan aiki ga kananan cibiyoyin kiwon lafiya.
Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari a ranar talat ta nuna bacin ran ta game da yanda kiwon lafiya mata masu juna biyu da yara kanana a kasar.
Uwargidan ta koka akan lamarin yayin da take kaddamar da katafaren asibitin mata masu juna biyu da yara wanda gidauniyar Aisha Buhari ta dauki nauyin gina a Daura nan jihar Katsina.
Tace lamarin ya tabarbare dalilin rashin ingantattun kayan aiki ga kananan cibiyoyin kiwon lafiya.
Tayi kira ga jama'a da masu ruwa da tsaki na kasar da su taimaka wajen wankar da kalubalen da mata ke fuskanta.
Daga karshe uwargidan shugaban kasa tace dalilin da ya sanya gidauniyar ta ta gudanar da aikin shine domin taimaka wa gwamnatin tarrayya wajen samad da tabbataciyar kulawa ta farko ga mara galihu a kasar
Aisha Buhari tace kulawa da lafiyar mata da yara kanana yana cikin ayyuka dake assasa cigaba.
Karanta >> Babu ko allurar sirinji a asibitin Aso Villa cewar Uwargidan shugaban kasa
Ita dai wannan cibiyar kulawa an gina ta ne cikin wata bakwai kuma ta samu kayan aiki na alfarma domin gudanar da ayyukan kula da lafiyar mai jinya kamar su gwaje-gwaje da tiyata domin rage yawan rashin lafiya ga masu juna biyu da mutuwar su yayin da suke neman haihuwa kamar yanda Aisha Buhari ta sanar.
Bisa ga kyautawan da take ga mara galihu a kasar, uwargidan shugaban kasa ta samu kyuata ta musamman daga matar gwamnan jihar Katsina Hajiya Zakiya Masari.