Kotun ta baiwa hukumar yan sanda da ta ICPC damar kama Herbert Wigwe kasancewar rashin zuwan shi ofishin hukumar ICPC bayan gayatar da hukumar wanda ke hana masu yi wa tattalin arziki zagon kasa tayi.
Kotun majistare dake nan garin Abuja ta bada izinin kama shugaban bankin Access tare da wasu ma'aikatan bankin masu ruwa da tsaki.
A labarin da jaridar Daily trust ta fitar kotun ta baiwa hukumar yan sanda da ta ICPC damar kama Herbert Wigwe kasancewar rashin zuwan shi ofishin hukumar ICPC bayan gayatar da hukumar wanda ke hana masu yi wa tattalin arziki zagon kasa tayi.
Taribo Zimuzu Jim na Kotun majistare ya bayar da wannan izini tare da bada damar kama wata ma'aikaciyar bankin mai suna Neka Agodu kasancewar sun sabawa doka gayatar da ICPT tayi.
A ranar alhamis 7 ga watan disamba ne hukumar ICPC ta kai karar jami'an bankin babban kotun tarayya dake Abuja bisa ga rashin amsa gayatar da tayi masu.
Su dai ma'aikatan sun shiga tarkon hukumar wanda ke hana almundahana bisa ga wani rashin kiyaye doka da aka kafa kan makurar cinikayar bankin.
Lamarin dai ya faru sanadiyar cinikin da wata kamfani Blaid construction Limited tare da Blaid Properties tayi.