Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya sanar da haka a taron da yan majalisar dattawa suka gabatar a jihar kano kan yunkurin yakar amfani da miyagun kwayoyi.
Gwamnatin jihar Kano tace ta halaka miyagun kwayoyi na kimanin biliyan N4.1 da ta kama a jihar bana.
Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya sanar da haka a taron da yan majalisar dattawa suka gabatar a jihar kano kan yunkurin yakar amfani da miyagun kwayoyi.
Gwamnan yace wannan yana cikin daya daga cikin matakin da gwamnatin sa ta dauka wajen yakar amfani da miyagun kwayoyi a jihar.
A taron wanda mataimakin sa Farfesa Hafiz Abubakar ya wakilce shi, Ganduje yace an kama miyagun kwayoyin a sassa daban daban na fadin jihar daga hannun masu safarar su yayin da suke yunkurin shigowa dasu.
Ganduje yace yawan amfani da miyagun kwayoyi a jihar yayi kumari domin ya wuce gona da iri fiye da yadda gwamnati take tsammani.
Karanta labarin>> Gwamnan jihar kano ya sha da ƙyar harin da ƴan fashi suka kai mai
yace yakin kawar da wannan kalubalen yana bukatan taimakon gwamnatin tarayya domin gwamnatocin jihohi bata iya gudanar da yunkurin ita kadai.
Bisa ga wannan yakin da gwamanti ke yunkuri yi wata kwararriyar likita tayi kira na a haramta sayar da magungunan tari don kawar da illar da take haifarwa a al'umma.
Bisa ga wannan manufar gwamnatin sa ta kafa kwamiti ta musamman domin yada wannan manufar har ma ya kara da cewa suna iya bakin kokarin su wajen gudanar da haka.
Daga karshe gwamnan ya jinjina ma yan majalisar dattawa bisa ga shirin kirkiro taro kan wannan batu wanda ke kalubalantar alúmmar Nijeriya. Bugu da kari ya nuna farin cikin sa ga shugaban majalisar Bukola Saraki kan zabar jihar Kano a matsayin inda aka gudanar da taron.
Jama'a da dama suka halarci wajen taron daga jihohi daban daban na fadin kasa.